Guidance

Notice of rights and entitlements Hausa (PACE Code C) (accessible version)

Updated 27 January 2020

Ka tuna hakkokin ka a yayin da ka ke a tsare

Wadanan hakkokin suna a tabbacin lamuni karkashin dokar Ingila da Yankin Wales kuma an bi tsarin dokar yarjejeniyar na kasashen Turai na EU 2012/13 akan 鈥榶ancin samun bayanai a tsarin hukunta laifuka.

An takkaita hakkokin ka a ofishin yan鈥檚anda a wannan shafin littafin.Akwai Karin bayanai a sakin layi da daya zuwa na goma sha daya a shafin littafi na gaba.Cikakken bayanai suna tsarin dokokin al鈥檃du na yansanda na C

  1. Ka gaya wa 鈥榶ansanda in kana son lauya ya taimake ka yayin da ka ke cikin ofishin 鈥榶ansanda. Ba sai ka biya kudi ba.
  2. Ka gayawa 鈥榶ansanda idan kana son a gaya wa wani cewa kana ofishin 鈥榶ansanda. Ba sai ka biya kudi ba.
  3. Ka gayawa 鈥榶ansanda idan kana son ganin dokokinsu 鈥 Ana kiransu tsarin dokokin al鈥檃du
  4. Ka gayawa 鈥榶ansanda idan kana son a yi maka magani wata cutar da ked a mun ka. Ka kuma gaya ma yan鈥檚anda idan baka jin dadin jikin ka ko kuma ka ji ciwo.Samun magani kyauta ne ba sai ka biya ba. .
  5. Idan aka tambayeka game da wani laifi da ake zargin ka akai, ba dole ba ne ka yi Magana. Sai dai kuma, hakan zai iya yin illa game da kariyar ka idan ba ka ambaci abin da aka tambayeka ba wanda daga bisani za ka dogara da shi a kotu. Za a iya bayar da duk abin da ka fada a cikin hujjar laifinka.
  6. Dole ne 鈥榶ansanda su yi maka bayanin laifin da suke ganin ka aikata da dalilin kama ka da kuma tsare ka da aka yi.
  7. Dole ne 鈥榶ansanda su baka ko lauyanka damar ganin rubutattcan bayanai da takardu game da dalilin kama ka da tsare ka da aka yi da kuma game da lokacin da za ka shafe a ofishin 鈥榶ansanda.
  8. Dole ne 鈥榶ansanda su samo maka mai fassara, in kana bukata. Haka kuma za a iya fassara maka wasu takardun bayanai. Ba sai ka biya kudi ba.
  9. Gayawa 鈥榶ansanda idan kai ba dan Birtaniya ba ne kuma idan kana son tuntubar ofishin jakadancin kasarku ko karamin ofishin jakadanci ko kuma kana son a gaya musu cewa kana tsare. Ba sai ka biya kudi ba.
  10. Dole ne 鈥榶ansanda su gaya maka na tsawon lokacin da za su iya tsare ka.
  11. Idan aka tuhume ka kuma shari鈥檃rka ta je kotu, kai ko lauyanka na da 鈥榶ancin ganin hujjar bangaren kara kafin kotu ta fara sauraron karar.

Idan baka tabbattar da wadannan hakkokin ba , ka gaya wa hafsan yan鈥檚anda

Ka duba shafin takaitawa na littafin domin Karin bayani akan yadda yan鈥檚anda suke bi da kai, kuma kula da kai

Wannan Sigar Sanarwar Hakkoki da Da鈥 aowi ya fara aiki ne daga biyu ga watan 21 Agusta 2019

Ka tabbatar ka ajiye wannan bayanai kuma ka karanta su da wuri . Zasu taima keka, yanke shawara a lokacin da ka ke ofishin yan sanda.

1. Samun lauya ya taimake ka

  • Lauya zai iya taimakon ka da bada shawara akan doka.
  • Neman magana da lauya ba shi zai sa a kama ka da laifi ba.
  • Yan鈥檚anda dole sai ya tambaye ka ko kana bukatar shawar dokoki daga lauya..
  • Dole ne yan sanda su tabbatar sun barka ka yi magana da lauya a kowani lokaci kake bukata,dare ko rana lokacin da kake ofishin yansanda.
  • Idan ka riga ka tambayi shawaran dokoki, yan鈥檚anda basu da galiban su yi maka tambayoyi,har sai ka samu yin magana da lauya. Idan yan鈥檚anda sun yi maka tambaya,zaka iya ce wa kana bukatar lauya a dakin.
  • Idan ka gaya wa yan鈥檚anda ce wa ba ka bukatar shawar dokoki daga wurin lauya ka zo da baya ka sa ke shawara ,ka gaya wa hafsa yan鈥檚anda, saboda a taimake ka a samu maka lauya.
  • Idan lauya bai zo ba,ko kuma bai tuntube ka ba a ofishin yan鈥檚anda,ko kuma kana bukatar lauya kuma,ka gaya wa yan鈥檚anda su tuntube maka lauya kuma.

Shawarar da lauya ke bayarwa akan wasu abubuwa da basu da nauyi sosai da ba tare da ka biya kudi ba:

  • Akan shawarar da basu da nauyi sosai,shawarar da ake yi a kyauta daga Mma鈥檃ikatar kare laifufuka(CDS) kai tsaye ne zasu bada shawara ta talho kawai to sai dai inda aka bada wani sharadi kan lokacin da ya kamata lauya ya zo, kamar cewa:
    • 鈥榊an sanda na son yi maka tambayoyi akan wani laifi ko kuma kana cikin wanda za鈥檃 shaida a jerin layin jama鈥檃 don shaida mai laifi.
    • Kana bukatar taimako daga鈥 mutumin da ya cancanta鈥. Ka dubi wurin da aka ce 鈥渕utanen dake neman taimako鈥.
    • Ko baka iya yin wata magana a wayar tarho,ko kuma
    • 鈥榊an sanda sun zarge ka da aikata wani babban laifi

A lokacin da ba SAI KAWAI TA WAYAR TARHO za鈥檃 baka shawara ba tare da biyan kudi ba daga Jami鈥檃n MA鈥橝IKATAR kare LAIFUKA (CDS):

  • Zaka iya neman yin magana da Lauyan da ka sani kuma ba sai ka biya kudi ba idan suna aikin bada taimako ta fuskar sharia.Idan baka san wani Lauya ba, ko kuma ba鈥檃 iya tuntubar Lauyan da ka sani, Zaka iya magana da Lauyan dake aiki anan.Ba sai ka biya kudi ba.
  • Babu wata mu鈥檃mulla tsakanin Lauyan dake aiki anan da kuma 鈥榶an sanda.

Idan za鈥檃 shirya baka shawara ta fuskar shari鈥檃 ba tare da ka biya ba.:

  • 鈥榊an sanda zasu tuntubi Cibiyar da ake neman Lauya mai karewa (DSCC). Cibiyar da ake neman Lauya mai karewa (DSCC) zata shirya irin shawarar da za鈥檃 bayar ta fuskar shari鈥檃 ko dai daga Cibiyar da ake nemanLauya mai karewa kai tsaye (CDS Direct),ko daga Lauyan da ka nema ko kuma daga Lauya mai aiki anan.
  • Su Cibiyar da ake neman Lauyan mai kariya(DSCC) da Lauya mai karewa kai tsaye (CDS Direct) cibiyoyi ne masu zaman kan su dake da alhakin shirin bada shawara ta fuskar shari鈥檃 ba tare da biyan kudi ba sannan kuma babu ruwansu da 鈥榶an sanda.

Idan kana son ka biya lauyan da kanka:

  • A dukkan hali zaka iya ka biya kudi domin samun shawara daga lauya akan dokoki
  • Idan har shawarar lauyan ba ta wuce ta tarho ba daga Lauya mai karewa kai tsaye (CDS Direct) ,zaka iya magana da Lauyan da ka zaba ta wayar tarho idan kana so amma kuma ba za鈥檃 biya su ba,ta hanyar taimakon da ake bayarwa ta fuskar sharia sannan kila su tambaye ka don ka biya su. Cibiyar da ake neman Lauyan mai karewa (DSCC) zata tuntubi Lauyan ka a madadin ka.
  • Kana da 鈥榶ancin tattaunawa a kebe ta wayar tarho tare da Lauyan da ka zaba ko kuma zai yanke shawarar zuwa ganin ka a ofishin 鈥榶an sanda.
  • Idan har ba鈥檃 iya tuntubar Lauyan da ka zaba ba, har wa ila yau 鈥榶an sanda zasu iya kiran. Cibiyar da ake neman Lauyan mai karewa (DSCC) domin a shirya Lauyan dake aiki anan ya baka shawara ta fuskar shawarwari ba tare da ka biya kudi ba.

2. Gaya wa wani kana Ofishin 鈥榶an sanda

  • Zaka iya gayawa 鈥榶an sanda su tuntubi wani wanda ya kamata ya sani cewa kana ofishin 鈥榶an sanda.Ba sai ka biya kudi ba.
  • Zasu tuntubi wani a madadin ka da zaran sun samu damar yin hakan.

3. Duba tsarin dokoki

  • Tsarin Dokoki wasu dokoki ne dake gaya maka abin da 鈥榶an sanda zasu iya yi ko kuma ba zasu iya yi ba,a yayin da kake ofishin 鈥榶an sanda.
  • 鈥榊an sanda zasu kyale ka don ka karanta Tsarin Dokokin,amma kuma ba zaka iya daukar tsawon lokaci ba,don karantawa har ya kawo jinkiri ga 鈥榶ansanda wajen gano cewa ko ka karya doka.
  • Idan kana son karanta Tsrain Dokokin,sai ka gayawa Jami鈥檌n 鈥榙an sandan dake tsare da kai.

4. Ka gaya wa yansanda idan kaji ciwo ko baka da lafiya

  • Ka gayawa 鈥榶an sanda idan baka da lafiya ko kuma kana bukatar magani. Zasu kira likita ko nas ko kuma wasu jami鈥檃n kula da lafiya kuma ba za ka biya kudi ba.
  • Za鈥檃 iya kyale ka don ka sha maganin ka, amma sai 鈥榶an sanda sun duba tukuna. Yawanci sai Nas ta gan ka da fari, amma kuma 鈥榶an sanda zasu aiko da likita idan kana bukata. Zaka iya neman ganin wani likita amma kila sai ka biya.

5. 鈥橸ancin kin yin magana

Idan an maka tambayoyi akan abun da ake zargin ka da shi ,ba dole ba sai ka yi magana.

Amma kuma, wannan zai iya raunata kariyar ka idan baka fadi ba a lokacin da a ka tambaya ka abun,kuma daga baya a kotu ka koma ka dogara akansa.

Za a dauki duk shaida ga duk abinda ka fadi a mastayin shaida.

6. Samun bayani game da laifin da ake zarginka da aikatawa da sanin dalilin kama ka da kuma tsare ka da ake yi

  • Dole ne 鈥榶ansanda su yi mka bayani game da yanayin laifin da suke ganin ka aikata. Wannan ya hada da lokaci da kuma wurin da suke ganin an aikata laifin.
  • Dole ne 鈥榶ansanda su gaya maka dalilin da ya sa suke ganin ka aikata laifin da kuma dalilin da ya sa suka ga ya kamata su kama ka.
  • Yayin da ka ke ofishin 鈥榶ansanda, dole ne 鈥榶ansanda su gaya mana dalilinsu na tsare ka.
  • Kafin a yi maka kowace irin tambaya game da kowane irin laifi dole ne 鈥榶ansanda su yi maka tare da lauyanka cikakken bayani game da abin 鈥榶ansanda suke ganin ka aikata don ka kare kanka, amma ba a lokacin da hakan zai kawo cikas ga binciken 鈥榶ansanda ba.
  • Wannan ya shafi dukkan sauran laifukan da 鈥榶ansanda suke ganin ka aikata.

7. Ganin rubutattun bayanai da takardu game da kama ka da kuma tsare ka da aka yi

  • Yayin da aka tsare ka a ofishin 鈥榶ansanda, dole ne 鈥榶ansanda su:
    • Rubuta a cikin rubutaccen bayanin tsare ka, dalili da bukatar kama ka da kuma abin da ya sa suke ganin akwai bukatar a tsare ka.
    • Kai da lauyanka ku duba wadannan rubutattun bayanai. Dansandan da ke tsare da kai shi ne zai shirya wannan.
  • Wannan ya shafi dukkan sauran laifukan da 鈥榶ansanda suke ganin ka aikata.
  • Dole ne 鈥榶ansanda su baka ko lauyanka damar duba takardu da kayayyakin da za su taimaka maka wajen kalubalantar cewa kamun da aka yi maka yana kan doka da kuma tsare ka da aka yi.

8. Samun tafinta saboda taimaka maka da fassarorin wadansu takardu

  • Idan baka iya ko baka jin turanci, to 鈥榶an sanda zasu shirya wani wanda ke magana ko jin yarenka ya taimake ka. Wannan kyauta ne.
  • Idan kurma ne kai ko kuma kana da wata matsala wajen yin magana, 鈥榶an sanda zasu shirya wani mai tafinta da turanci daga masu tafinta ta hanyar nuni daga Ma鈥檃ikatar Magana ta nuni na Birtaniya don a taimakeka. Wannan kyauta ne.
  • Idan ba ka magana ko fahimtar Turanci, 鈥榶an sandan za su samo maka tafinta don gaya maka dalilin da ya sa suke tsare da kai da kuma game da duk wani laifi da ake tuhumarka. Wannan ya zama wajibi a yi shi a duk lokacin da 拼an sanda suke tsare da kai.
  • Bayan kowace shawara da aka yanke ta tsare ka kuma bayan an kama ka da wani laifi dole ne 拼an sanda su baka wani bayani cikin harshenka na dalilin da ya sa aka tsare ka da kuma laifin da aka same ka da shi, sai dai idan akwai wasu dalilai na musamman na kasa yin haka.Wa蓷annan su ne:
    • Idan ka yanke shawarar ba ka bu茩atar bayanin don kare kanka saboda ka fahimci abin da yake faruwa da kuma sakamakon rashin 茩in kar蓳ar ha茩茩inka na kar蓳ar bayani kuma 拼an sandan sun ba ka damar tambayar wani lauya don taimaka maka yanke shawara. Dole ne ka bayar da amincewarka a rubuce kuma.
    • Idan fassarar baki ko ta茩aitawa ta hanyar wani tafinta maimakon fassara a rubuce ta wadatar maka ka kare kanka kuma kana da cikakkiyar fahimta game da abin da yake faruwa kuma jami鈥檌n da yake tsare da kai ya bayar da izini da wannan.
  • Idan 鈥榶an sanda suka yi maka tambayoyi kuma ba ka yi rikodin maganar ba, mai yin tafinta zai rubuta wadannan tambayoyin da kuma amsoshinka a harshen da kake magana dashi. Zaka samu damar duba wannan kwafin ka sa hannu don tabbatar da cewa yayi daidai
  • Idan kana son yi wa 鈥榶an sanda bayani, mai tafinta zai dauki kwafin wannan bayanin a harshenka domin ka duba ka ga cewa yayi daidai.
  • Haka kuma kana da hakkin samun fassarar wannan Bayani. Idan ba a sami fassara ba, ya zama dole a yi maka bayani ta hanyar tafinta sannan a samar maka da fassara ba tare da jan lokaci ba.

9. Tuntubar ofishin jakadancin

Idan kai ba dan kasar Birtaniya bane, zaka iya gayawa 鈥榶an sanda cewa kana san tuntubar ofishin jakadancin kasarka domin gaya musu inda kake da kuma dalilin da ya sanya kake tsare a ofishin 鈥榶an sanda. Za su kuma iya ziyartar ka a kebe ko kuma su aika wani Lauya don ya zo ganinka

10. Har wani tsawon lokaci ne za鈥檃 iya tsare ka?

  • Yawanci ana iya tsare ka har tsawon sa鈥檕鈥檌 ashirin da hudu (24) ba tare da yi maka caji ba. Zai iya wuce haka,amma kuma sai dai kawai in wani Sufeton 鈥榶an sanda ko kuma kotu ta bada umurnin a yi hakan.Bayan sa鈥檕鈥檌 talatin da shida (36) kotu ce kawai zata kara ba 鈥榶an sanda Karin lokaci su tsare ka ba tare da an caje ka ba.
  • A ko da yaushe,dole ne wani babban jami鈥檌n 鈥榶an sanda ya duba maganar ka don ya ga cewa ko ya kama dole a tsare ka anan ofishin 鈥榶ansanda. Ana kiran haka sake-dubawa. Ana kiran wannan sake dubawa.Ka na da 鈥榶ancin yin magana akan wannan shawarar da aka yanke, sai fa idan baka da lafiya. Shi ma Lauyan ka, yana da ikon fadin wani abu game da wannan shawarar da aka yanke a madadin ka.
  • Idan jami鈥檌 mai sake-dubawa bai sake ka ba, to dole a gaya maka abin da ya sa da kuma dalilin da aka rubuta a rubutaccen bayanin tsare ka.
  • Idan tsare ka ba shi da muhimmanci to dole a sake ka. Idan 鈥榶ansanda suna son ci gaba da binciken laifin, za a iya sakin ka a kan beli.
  • Yayin da 鈥榶ansanda suka nemi kotu ta bada umarnin cigaba da tsare ka:
    • Dole ne a kawo ka kotu don sauraron tuhumar.
    • Dole ne a baka kwafin bayanin da aka gabatarwa kotu game da hujjar laifin da kuma dalilin da 鈥榶ansanda suke son cigaba da tsare ka.
    • Kana da 鈥榶ancin lauya ya kasance tare da kai a kotu.
    • Za a baiwa 鈥榶ansanda damar tsare ka ne kawai idan kotu ta gamsu cewa hakan ya zama dole sannan da cewa 鈥榶ansandan suka tsakiyar binciken lamarinka a nutse ba tare da bata lokaci ba.
    • yan sanda baza su barka a tsare ba, sai dai in kotu ta ga haka ya dace da kuma da ci gaba da binciken lefin ka da sauri, ba tare da bacin lokaci ba.
  • Idan 鈥榶ansanda suka da isassun hujjojin da za su tura ka zuwa kotu, za a iya tuhumarka a ofishin 鈥榶ansandan ko kuma ta hanyar sakon gidan waya, don ka bayyana a kotu inda za a yi maka shari鈥檃.

11. Damar ganin hujjar laifi idan shari鈥檃rka ta je kotu

Idan aka tuhume ka da wani laifi, dole a baka ko lauyanka damar ganin hujjojin laifinka da kuma hujjojin da za su iya taimaka maka wajen kare kanka. Dole ne a yi wannan kafin a fara shari鈥檃rka. 鈥榊ansanda da kuma Hukumar Gabatar da tuhuma ta Sarauniya suke da alhakin shirya wannan da kuma samar da damar ganin takardun da kayayyakin da suka jibanci tuhumar.

Wasu abubuwan da ya kamata ka sani kan zama cikin ofishin 鈥榊an sanda

Yadda ya kamata a kula da kai da kuma dawainiyarka

Wadannan takaittun bayanai ne akan abin da ya kamata ka yi la鈥檃kari dasu yayin da kake ofishin 鈥榶an sanda. Idan kana son Karin bayani,sai ka nemi ganin Tsarin Dokoki. Sun kunshi jerin sunayen inda zaka samo karin bayanai akan wadannan abubuwa. Ka tambayi Jami鈥檌n dan sanda dake tsare da kai idan kana da wasu tambayoyi.

Mutanen dake Bukatar Taimako

  • Idan shekarun ka basu wuce goma sha takwas ba (18) ko kana da matsalar kaifin kwakwalwa, misali tabin hankali ,to dole ne ka samu wani ya kasance tare da kai a lokacin da yan鈥檚andan ke yin wasu abubuw. Ana kiran wannan 鈥渕utumin da ya cancanta鈥, kuma za a ba su kwafi na wannan Bayani.
  • Dole ne wannan mutumin da ya cancanta ya kasance yana tare da kai a lokacin da 鈥榶an sanda suke fada maka 鈥榶ancin ka da kumadalilin da ya sanya aka tsare ka a ofishin 鈥榶an sanda. Dole shi ko kuma ita ta kuma kasance ko ya kasance yana tare da kai a lokacin da 鈥榶an sanda ke karanta maka gargadin.
  • mutumin da ya cancanta zai kuma iya neman Lauya a madadinka .
  • Zaka iya tambayar Lauyanka ba tare da mutumin da ya cancanta a dakin ba idan kana son yin hakan.
  • Kuma kila 鈥榶an sanda su bukaci yin daya daga cikin abubuwan da aka lissafa a kasa yayin da kake ofishin 鈥榶an sanda. Dole mutumin da ya cancanta, ya kasance yana tare da kai a duk tsawon lokaci sai dai kuma idan akwai dalilai na musamman, idan 鈥榶an sanda suka yi kowane abu daga cikin wadannan abubuwan:
    • Su dauki hoto ko yi maka tambayoyi ko kuma neman ka don ka sa hannu a wani jawabin da aka rubuta ko kuma bayanan 鈥榶an sanda.
    • Cire tufafin ka domin a bincike ka.
    • Dauki hoton yatsunka, hoto ko DNA ko kuma wani gwajin.
    • Ka shiga layin jerin mutane da ake yi da nufin samun shaida.
  • Za a bada dama ga cikakken mutuminka don ya zo da kansa ko kuma ta waya,I dan mutumin da ya cancanta na wurin,to dole ne kuma ya kansance yana wurin idan 鈥榶an sanda suka.
  • Idan cikakken mutuminka yana nan, dole ne su kasance a wurin lokacin da 鈥榶ansanda suka tuhume ka da laifi.

Samun bayanin lokacin da kayi a ofishin yan sanda

  • Duk abun da ya same ka a lokacin da kake ofishin yan san da yana a rubuce a littafi wanda a ke kira maigadin rikodi.
  • Bayan ka bar ofishin yan sanda ,kai,ko lauyar ka,ko mutumin day a cancanta za ya iya tambayar kwafi na custody rikodi din. Yan sanda za su baka kwafin na custody record da wurwuri.
  • Za ka iya tambayar yan sanda sub aka kwafi na custody rikodi din har na madadin wata goma sha biyu bayan ka bar ofishin yan sanda. Zaka iya tambayi yansanda akan mai gadin rikodi (Takarda) a tsawon wata sha biyu, bayan ka bar wajen su.

Sanar da wani

  • Bayan magana da Lauya da kuma sanar da wani cewa an tsare ka, yawanci za鈥檃 bar ka, kayi amfani da wayar tarho sai daya.
  • Ka tambayi 鈥榶an sanda idan kana son ka yi waya.
  • Kuma zaka nemi a baka alkalami da takarda.
  • Za鈥檃 kuma iya kyalewa don a ziyarce ka amma kuma Jami鈥檌n dake tsare da kai zai iya hana yin hakan.

Gadurun dinka

  • Idan ya yiwu,dole ne a ajiye ka a gadurun kai kadai.
  • Dole ne ya zamana da tsabta, da dumi da kuma haske.
  • Dole zannuwan gadon su zamana da tsabta kuma a gyare.
  • Dole a kyale ka don ka yi amfani da bayangida sannan kuma ka yi wanka.

Bukatu na kai- Lafia, tsabta da jindadin

  • Dole ne a tambaye ku idan kuna son yin magana cikin sirri tare da membobi na ma鈥檃ikatan tsaro game da duk wani kebebben bukatun da ya danganci lafiyar ku, tsabta da walwala da za su iya shafanku ko damun ku yayin da kuna a tsare.
  • Yan sanda za su shirya samar da kayayyakin da aka ga sun dace don biyan bukatun ku. Idan kanaso, mutumin da zakuyi magana da shi ya kasance jinsi daya da kai.
  • Idan ke mace ce yar shekaru goma sha takwas (18) ko sama da haka, dole ne a tambaye ku idan kuna bukatar ko akwai yiwuwar kuna bukatar kowane samfuran na tsaron jinin haila yayin da kake a tsare kuma dole ne a gaya muku
    • za a samar da kayayyakin haila a kyauta
    • Akwai kayayyakin maye gurbin wasu ; da
    • Iyalanku ko abokanku na iya ba ku kayayyakin a kan kudin su idan jami鈥檌n tsaro ya amince
  • Idan ke budurwa ce 鈥榶ar shekara goma sha takwas (18), jami鈥檌n tsaro zai tabbatar da cewa wata mace a ofishin鈥 yan sanda tana nan don ta kula da ke kuma zata tambayeki game da bukatunki da kayayyakin haila.

Tufafi

Idan an dauki kayan ka daga hannunka,to dole 鈥榶an sanda su baka wasu tufafi.

Abinci da Sha

Dole a baka abinci sau 3 a rana tare da abin sha.Kuma zaka iya samun abun sha a tsakanin lokuttan da ake baka abinci.

Motsa jiki

Idan ya yiwu,dole a kyale ka don fita waje a kowace rana don shan iska.

Idan 鈥榶an sanda sun tambayeka

  • Dole dakin ya zama da tsabta,da dumi da kuma haske.
  • Ba dole bane ka tashi tsaye.
  • Dole Jami鈥檃n 鈥榶an sanda su gaya maka sunayensu da mukaminsu.
  • Dole ne a bar ka samun walwala a lokuttan cin abinci da kuma samun shan ruwa bayan kimanin sa鈥檕鈥檌 biyu.
  • Akalla dole a barka don ka huta har tsawon sa鈥檕鈥檌 8 a cikin sa鈥檕鈥檌 24 da ake tsare da kai.

Bukatun Addini

Gaya wa 鈥榶ansanda idan kana bukatar kowane irin abu da zai taimaka maka gudanar da addininka yayin da ka ke ofishin. Za su iya samar da littattafan addini da sauran abubuwa, da suka masu muhimmanci.

Lokuttan da dokokin da aka sani suka banbanta

Samun Lauya don ya taimakeka

Akwai wasu lokutta da ya kamata 鈥榶an sanda su yi maka tambayoyi da gaggawa kafin kayi magana da Lauya. An bada bayanan wadannan lokuttan na musamman a Tsarin Dokoki. Wannan littafi ya tsara abubuwan da 鈥榶an sanda zasu yi ko kuma ba zasu iya yi ba, yayin da kake tsare a ofishin 鈥榶an sanda. Idan kana son ka duba bayani,suna cikin sakin layin na 6.6 na tsarin na dokoki na C na Tsarin Dokoki.

Akwai wani lokaci na musamman da 鈥榶an sanda ba zasu kyale ka, yin magana da Lauyan da ka zaba ba. Idan haka ya faru, to dole ne a kyale ka don ka zabi wani Lauya. Idan kana son duba bayanai, yan cikin jerin bayanai a jerin B na Code C na tsarin Dokoki.

Gayawa wani cewa kana Ofishin 鈥榶an sanda

Akwai wasu lokutta na musamma da 鈥榶an sanda ba za su kyale ka tuntubi kowa ba. An bada bayanan wadannan lokutta na musamman a Tsarin Dokokin. Idan kan son duba bayanai, a jerin bayanai suna jerin B na tsarin dokokin C na tsarin Dokoki.

Daukar gwajin numfashi

Idan aka kama ka saboda laifin yin tuki a lokacin da kake buge da shan giya, kana da 鈥榶ancin yin magana da Lauya. Wannan 鈥榶ancin baya nufin cewa zaka iya hana 鈥榶an sanda daukar gwajin numfashin ka, ko jinni ko fitsari ko ma kafin kayi magana da Lauya ba.

Tsarewa a karkashin Dokar da ta shafi tabin hanakali na 1983

Kuma 鈥榶an sanda zasu iya tsare mutane a wani ofishin 鈥榶an sanda domin a duba ka, a karkashin Dokar Tabbin Hankali. Idan aka tsare ka a karkashin Dokar da ta shafi Tafin Hankali, wannan baya nufin an kama ka ne don ka aikata wani laifi .

Hakan ya nuna cewa dole ne 鈥榶an sanda su shirya maka ganin wani Likita da kuma wani kwararren Likitan tabbin hankali don ya yi bincike. Dole ne a duba ka cikin sa鈥檕鈥檌 saba鈥檌n da biyu (24) ko kwana ukwu (12) da isowar ka cikin ofishin 鈥榶an sanda amma kuma 鈥榶an sanda zasu yi kokarin shirya yin hakan bada wani bata lokaci ba. A wannan lokacin 鈥榶an sanda zasu iya maida ka wani wurin da ya dace domin a samu damar yi maka bincike.

A yayin da kake jiran a yi maka binciken, 鈥榶an sanda zasu iya shirya ka don ganin wani ma鈥檃ikacin kiwon lafiya da aka amince.Ba zasu iya yin binciken ba amma kuma zasu iya taimakon ka da wasu matsalolin da suka dame ka game da lafiyarka kuma su taimaka wajen yi maka bayani akan abinda yin binciken yake nufi.

Masu ziyara dake zaman kansu

Akwai wasu mutane na kungiyar jama鈥檃 da ake barin su tafi ofisoshin 鈥榶an sanada bada wata sanarwa ba. Ana kiransu masu ziyarar kurkuku dake zaman kansu kuma suna aiki ne ba don kudi ba domin tabbatar da cewa mutanen da aka daure an yi musu adalci sannan kuma suna da ikon samun abin da ke 鈥榶ancinsu.

Ba dole bane ka ga mai ziyara dake zaman kansa, sannan kuma ba zaka nemi wani mai ziyara dake zaman kanshi ya ziyarce ka ba.Idan wani mai ziyara dake zaman kanshi ya ziyarce ka yayin da kake daure, zai so gane ko an kare lafiyarka da kuma 鈥榶ancinka don ya gamsu ba tare da hannun 鈥榶an sanda ba. Amma kuma ba dole bane ka yi magana dasu idan baka so.

Yadda zaka kai kara

Idan kana son ka kai kara ga halin da aka nuna maka, ka nemi yin magana da jami鈥檌n 鈥榶ansanda wanda yake sufeto ne ko kuma mai wani babban mukami. Bayan an sake ka, zaka iya kai kara wani ofishin 鈥榶an sanda,ko Hukumar kai kara ta 鈥榶ansanda mai zaman kanta(IOPC) ko ta wurin Lauyan ka ko kuma dan Majlisar ka a madadin ka